Shugabanni a Najeriya sun yi Allah wadai da tagwayen hare-haren Kaduna
July 24, 2014Kasa da awoyi 24 da kai hari kan babban madugun adawa na siyasar tarrayar Najeriya Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, jam'iyyarsa ta APC ta zargi gwamnatin kasar da kokarin rushe adawa ko ta halin kaka.
Ya dai kai ga fadar albarkacin bakinsa komai daci, amma kuma ya ga barazana mafi girma a cikin shekaru 12 na siyasarsa. A farkon makon da muke ciki ne dai Buharin ya kai ga gargadi ga shugaban kasar da takawa sannu a cikin yunkurinsa na murkushe adawa ko ta halin kaka, abun kuma da ya kai ga martani mai zafi daga fadar gwamnatin kasar ta Aso Rock, da ta ce Buharin na kokari na shafa kashin kaji ga malafa ta shugaban kasar a halin yanzu, kafin daga baya a kai ga sabon harin da ya kai ga tada hankula cikin kasar.
To sai dai kuma a fadar Senata lawalli Shu'aib da ke zaman mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, sabon hari bisa jagoran sauyin kasar ta Najeriya bai isa sauya gugguwar da ke kadawa yanzu kuma ke neman tabbatar da sauyin a karon farko ba
“Ana son a kashe adawa, ana son ya kasance in ka na dan adawa kar ka motsa. Ka basu damar yin abun a suke so. Ka duba kaga mutanen da ake kaiwa hari. Yanzu an kai kul an kaiwa Janar Buhari hari to wa ya rage. Mu baza a hana mu siyasa ba, ba za'a hana mu shiga zabe ba. Kuma zamu dauki matakin da ba za'a hana mutane fitowa su jefa mana kuri'a ba. Yau in ka kasa Najeriya hudu kashi uku sun tsani PDP sun tsani gwamnatin PDP".
Ya zuwa yanzu dai harin na Buharin na shirin tabbatar da zargin makisan da a baya tsohon shugaban kasar ya ce sun horu da nufin tabbatar da karshe ga masu ja da Abujar da ke kara nuna alamun maitar ta a fili ya zuwa ga lashe zabukan kasar dake tafe.
Mawallafi: Ubale Musa
Editor: Pinado Abdu Waba