1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban ƙasar Yemen ya ce zai koma ƙasarsa

August 16, 2011

Shugaba Ali Abdallah Saleh wanda ke yin jinya a Saudiyya ya yi kira ga yan' adawar da su halarci zaɓɓuɓukan da za a gudanar a ƙasar

https://p.dw.com/p/12I0J
Ali Abdallah SalehHoto: AP

Shugaba  Ali Abdallah Saleh  na ƙasar Yemen wanda ke murmure wa daga rauni da ya samu a ƙasar Saudiyya inda ya ke yin jinya ya yi alƙawarin  sake koma ƙasar sa nan ba da daɗewa ba.A cikin wani jawabi da yayi ta gidan telbijan da aka watsa kai  tsaye a birnin Sanaa  hed  kwatar ta Yemen.

Shugaba Saleh ya yi kira ga yan' adawar da su halarci zaɓɓuɓukan da za a gudanar domin kawo ƙarshen ƙangi na al'amuran siyasa da ƙasar ke fuskanta kusan watannin bakwai. A cikin watan yunin da ya gabata ne shugaban ya samu rauni bayan da wata bam ta fashe a fadar sa.Shugaban ya kuma ce a hirye ya ke ya bar mulki amma ta hanyar yin zaɓe ba yin juyin mulki ba.Shugaba Saleh wanda ya ƙwashe kusan shekaru 33 kan karagar mulki a karo na ukku jere kenan ya ke ƙin sa hannu akan wata yarjejeniya tare da ƙungiyar ƙasashen yankin Golfe domin kafa wata gwamnatin riƙon ƙwarya.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita       : Zainab Mohammed Abubakar