1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Wikileaks Julian Assange ya shaki iskar yanci

Binta Aliyu Zurmi
June 26, 2024

Dan jaridar nan kuma shugaban Wikileaks Julian Assange a wannan rana ta Laraba ce ya shaki iskar yanci kuma tuni ya kama hanyarsa ta komawa gida Australiya bayan shafe shekaru 14 a gidan kason Birtaniya.

https://p.dw.com/p/4hW68
USA | Gericht WikiLeaks-Gründer Julian Assange
Hoto: Kim Hong-Ji/REUTERS

Julian Assange mai shekaru 52 ya gurfana a gaban wata kotun Amirka bisa tuhuma a kan zargin bankado wasu bayanan sirrin tsaron kasar, bayan samunsa da laifi kotu yanke masa hukuncin zaman kaso na shekaru biyar amma kuma an yi masa afuwa bisa shekarun da ya shafe a kurkukun Landon. 

Kungiyoyin 'yan jarida da dama ne suka shafe shekarui suna fafutukar ganin wannan rana ta zo, inda suka ce ci gaba da tsare shi kamar  yin karan tsaye ne ga aikin jarida da ma su kansu 'yan jaridar.


Assange ya kasance gwarzo ga masu kare yanci fadin albarkacin baki, kuma ya sha alwashin ci gaba da aikinsa na jarida. Lawyan shugaban na Wikileaks ya kira wannan rana a matsayin mai cike da tarihi da ta kawo karshen shekaru 14 na tirka-tirkar shari'a.