1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shugaban Ukraine Zelensky ya nemi a sulhunta su da Rasha

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 8, 2024

Mr Zelensky ya ce sojojin Ukraine dubu arba'in da uku ne suka mutu a fagen daga sanadiyyar yaki da Rasha tsawon shekaru uku.

https://p.dw.com/p/4ntI4
Shugaban Amurka mai jiran gado Trump da na Faransa Macron tare da na Ukraine Zelensky
Hoto: Sarah Meyssonnier/AFP

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky, ya ce sojojin kasar dubu arba'in da uku ne suka mutu a fagen daga, sanadiyyar yakin da yake yi da Rasha na tsawon shekaru uku, yayin da wasu dubu dari uku da saba'in suka samu raunuka.

Karin bayani:Amurka ta bukaci Rasha da Ukraine zama a teburin sulhu

Mr Zelensky ya wallafa wannan sako ne a shafinsa na sada zumunta na zamani, inda ya sanar da shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump da na Faransa Emmanuel Macron cewa a shirye yake don tattauna hanyoyin cimma sulhu da Rasha.