SiyasaGabas ta Tsakiya
Erdogan ya maka babban dan siyasar da ke adawa da shi a kotu
February 18, 2021Talla
Erdogan ya zargi Shugaban jam'iyyar adawa Kemal Kilicdaroglu da bata masa suna a kan batun kisan da Turkiyya ta ce mayakan Kurdawa sun yi wa 'yan kasar su 13 a arewacin Iraqi a makon da ya gabata.
Duk da cewa mayakan Kurdawan sun fito sun musanta zargin da Shugaba Erdogan ya yi musu amma maganar ta zama babban abin da 'yan siyasa ke tattaunawa a cikin Turkiyya, inda shi shugaban adawa Kemal ya zargi Erdogan da sakaci wurin kisan mutanen. Sai dai kuma a yanzu lauyoyin Shugaba Erdogan sun ce suna bukatar dan adawar ya biya Erdogan kudin da suka kai Euro 60,000 a matsayin diyyar bata masa suna da ya yi.