1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Tinubu na son a kara azama kan matsalolin Afirka

September 21, 2023

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta kara azama wajen magance matsalolin da suka addabi nahiyar Afirka na tsaro da fatara da talauci a Afirka

https://p.dw.com/p/4WfDq
Nigeria | Bola Tinubu
Najeriya I Bola Tinubu Hoto: Sunday Aghaeze/Nigeria State House via AP/picture alliance

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da sakatare janar na Majalisar Dinkin DuniyaAntonio Guterres, a daura da taron da yanzu haka ke gudana a New York din Amurka, kamar yadda mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya sanar.

Karin Bayani: Kwanaki 100 na gwamnati a Najeriya

Bola Tinubu ya kara da cewa wawure dukiyar Afirka da ma albarkatun karkashin kasa da wasu miyagun mutane ke yi ba bisa ka'ida ba zuwa ketare, na daga cikin abubuwan da ke kara haddasa rashin zaman lafiya a yankin.

Karin Bayani: Yunkurin dakile matsalar tsaron yankin Sahel

A na sa martanin sakatare janar na Majalisar Dinkin  Duniya Antonio Guterres, cewa ya yi akwai bukatar yin garambawul ga dokoki da tsare-tsare da za su ba da damar aiwatar da tsare-tsaren da za su ciyar da Afirka gaba da ma duniya baki-daya.