Shugaban Koriya ta Arewa na ganawa da shugaban China
May 8, 2018Talla
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya kai ziyara China inda ya gana da Shugaba Xi Jinping a karo na biyu. Kafofin yada labaran China sun ce an yi wannan ganawa ta ba zata a garin Dalian na yankin arewa maso gabashin kasar ta China.
Lamarin da yake zuwa gabanin ganawa da aka tsara tsakanin Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da kuma Shugaba Donald Trump na Amirka cikin makonni masu zuwa, game da neman hanyoyin dakile shirin kasar Koriya ta Arewa kan bunkasa makamun nukiliyar kasar.