Shugaban kasar Jamus ya yi kiran hadin kan al'umma
December 25, 2024Shugaban kasar ta Jamus Frank Walter Steinmeier ya yi amfani da jawabin da ya saba yi a bisa al'ada a duk ranar Kirsimeti wajen yin kiran hadin kai dangane da abubuwan da suka faru a kasar a baya bayan nan.
Sheinmeier ya fara jawabin nasa ne tare da yin tsokaci kan mummunan harin da aka afka da mota a kasuwar Kirsimeti a birnin Magdeburg a gabashin Jamus.
" Yace muna yi wa kowa barka da Kirsimeti a wannan lokaci. Sai dai bakar inuwa ta lullube Kirsimetin na bana cikin zaman makoki da alhini da ban tsoro. Yanayi na firgici da damuwa a game da abin da ya faru a Magdeburg yan kwanaki kadan kafin Kirsimeti. Na lura da dukkan wadannan daga jama'a da suka halarci taron addu'oi ga mutanen da suka rasu a harin. Muna mika ta'aziyya ga iyalai da aminan mutanen da suka rasu a wannan mummunan al'amari. Ana iya hasashe ne kawai irin bakin cikin da iyalansu suka shiga. Rayuwarsu ta sauya, abubuwan da suka tsara da fatan su da farin cikinsu an lalata su."
Steinmier ya kara da cewa wannan abin alhini ba mutanen da harin ya ritsa da su ne kadai suke jin radadinsa ba.
"Yace mutane da dama na jin bakin cikin wannan abu a wannan rana ta Kirsimeti. Mutane da dama za su ji babu dadi, watakila ma har da fargaba. Dukkan wannan yanayi abu ne da za a iya fahimta. To amma bai kamata mu bari ya rinjaye mu ko ya kassara mu ba. Fata na shi ne kada mu bari wannan abu ya sake faruwa. Mu hada kanmu. Hadin kai da aminci da kaunar juna su ne suka sa kasarmu ta zama yadda ta ke."
Da ya juya ga tasiri akan al'umma kuwa, Steinmeier ya yi kira ga mutanen Jamus da kada su rarraba.
"Yace akwai rashin gamsuwa kwarai akan siyasa da kasuwanci da dogon turanci kan rashin adalci. Furucin da jama'a ke yi a kasarmu ya yi tsauri, a wasu lokutan da nuna kiyayya a rayuwarmu ta yau da kullum.
Haka kuma shugaban gwamnatin na Jamus ya yi magana kan yakin da ake yi a Gabas ta Tsakiya da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Akwai kalubale masu yawa wadanda dole mu fuskance su. Ba za mu rika wurgi da su kamar wasu kyautukan da bama so ba. Dole ne mu fayyace gaskiya komai dacinta kan abubuwan da basu dace ba da abubuwan da basa tafiya daidai a kasarmu. Sannan kuma dole ne mu yi magana akan abin da ya kamata a yi cikin gaggawa."
Ya kuma yi tsokaci kan zaben da za a yi a Jamus a ranar 25 ga watan Fabrairun 2025. Yace yana da yakini a kan dimukuradiyya da dokoki da kuma kundin tsarin mulkin Jamus da ake amfani da shi tun 1949. Yace rushewar gwamnatin Jamus ba shi ne karshen duniya ba.
"Ya ce ko da gwamnati ta kawo karshe bakatatan kafin cikar wa'adinta, wannan ba shi ne karshen duniya, amma yanayi ne da za a koma a ga me kundin tsarin mulki ya ce akan haka. Zan yanke hukunci akan rushe majalisar dokoki da kuma sabon zabe cikin tsanaki bayan Kirsimeti".
Shugaban gwamnatin na Jamus ya kuma mika sako ga matasan kasar, inda yace ana bukatar su matuka a wurare da dama. Yana mai cewa matasan Jamus na iya yanke hukunci kan tafarkin rayuwarsu.