Tarihin Shugaban kasar Jamus da aka sake zaba
February 13, 2022Steinmeier ya dau kasada kuma ya yi nasara, ya sami amincewar dukkan jam'iyyun kawancen gwamnati SPD da FDP da kuma Greens hatta yan ra'ayin rikau CDU/CSU sun furta amincewa ta goyon bayansa basu tsayar da wani dan takara domin gogayya da shi ba. Armin Laschet shugaban jam'iyyar CDU yace musamman a wannan lokacin da ake ciki, kasar mu na bukatar mutum mai karfin fada a ji wanda ke hada kan jama'a ba mai raba su ba.
A lokacin wa'adin mulkinsa na shekaru biyar Frank-Walter Steinmeier ya sha nuna cewa yana son zama mai hada kan 'yan kasa kuma mai shiga tsakani.
Frank-Walter Steinmeier ya dade yana gudanar da zauren tattaunawa da kungiyoyin jama'a ciki har da masu tsattsauran akida AfD kan al'amuran da suka shafi kasa kamar lokacin annobar corona da ta buwayi kowa.
Frank-Walter Steinmeier mutum ne na gari kuma shugaban kasar da ake girmamawa. A farkon watan Janairun 2022 an yi wata tattaunawa a fadar shugaban kasar akan alfanu ko rashin alfanun tilasta wa jama'a yin allurar rigakafin corona. Haka kuma an gayyaci masu nuna shakku ko wadanda ke adawa da rigakafin a wajen tattaunawar wadda aka yi a baiyanar jama'a. An tafka muhawara mai zafi to amma shugaban kasar da aka nemi ra'ayinsa sai ya ce shi na kowa ne a saboda haka ba zai dauki matsayi akan wannan ba.
Frank-Walter Steinmeier ya kai matakin kololuwa a rayuwarsa ta siyasa a farkon shekarar 2017. A watan Fabrairun wannan shekarar aka zabe shi shugaban kasa da sakamako mai armashi.
Steinmeier ya dace da jam'iyyarsa ta SPD iyayensa ba masu hali ba. Mahaifinsa Kafinta ne da ya fito daga Detmold a yammacin Jamus. Ya yi digiri a fannin shari'a sannan ya yi digirin digirgir a dai wannan fanni kuma ya hadu da wacce ta zama matarsa a Jami'a Elke Büdenbender wadda ita ma lauya ce.
Steinmeier ya ja hankali tare da samun tausayawar Jamusawa bisa wani hukunci da ya yanke na radin kai inda a shekarar 2010 ya bai wa matarsa da ke fama da rashin lafiya a wancan lokaci kodarsa guda. Wannan ya ja hankalin kasa baki daya da suka tausayawa dan siyasar wanda ya har yau ya kasance mai saukin kai.
Steinmeier zai fara wa'adi na biyu a matsayin shugaban kasa yana da shekaru 66 a duniya. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a watan Janairu ta nuna kashi 86 cikin dari na Jamusawa sun ce yana aikinsa da kyau. Yayin da kashi 81 cikin dari kuma suka ce ya kamata ya cigaba a karagar mulki.
Kamun kansa shi ne jarinsa mai yiwuwa a wannan wa'adi na biyu da zai yi na shekaru biyar ya kasance gwarzon kasa mai hangen nesa.