Shugaban Brazil ya ketare rijiya da baya
August 3, 2017Shugaba Michel Temer na Brazil ya ketare rijiya da baibai bayan da ya yi nasarar samun rinjaye a kuri'ar da 'yan majalisar dokokin kasar suka kada kan batun gurfanar da shi a gaban kotun kolin kasar a bisa zargin cin hanci. 'Yan majalisar 263 ne daga cikin 513 da majalisar ta kunsa suka kada kuri'ar kin yin watsi da bukatar gurfanar da shugaban, alhali 'yan adawar kasar na bukatar samun kashi biyu daga cikin uku wato kuri'u 342 daga cikin 513 domin samun hurumin cimma burin nasu.
A wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na gwamnatin kasar jim kadan bayan bayyana sakamakon kuri'ar Shugaban Michel Temer ya bayyana farin cikinsa da nasarar da ya samu ida ya ce ''majalisa wacce ita ce wakiliyar al'umar Brazil ta bayyana matsayinta wanda ba ja a cikinsa kuma wannan nasara ba tawa ba ce, nasarar kasa ce da kuma demokradiyya".
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin watanni biyu da shugaba Michel Temer mai shekaru 76 da kuma ake zargi da cin hanci na Euro dubu 140 daga kamfanin sarrafa kayan nama na JBS ke ketara siradin shirin yankan kaunar kujerar mulkinsa.