1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin na Rasha ya isa a ƙasar Marokko.

September 7, 2006
https://p.dw.com/p/BukX

Shugaba Vladimir Putin na ƙasar Rasha, ya isa a birnin Casablanca na ƙasar Marokko ya da safen nan, a wata ziyarar farko da wani shugaban Rashan ya taba kaiwa a ƙasar tun 1961.

Firamiyan Marokkon, Driss Jettou ne ya tarbi shugaba Putin yayin da ya sauka a birnin Casablancan daga Afirka Ta Kudu.

A yau ɗin ne dai ake sa ran zai gana da Sarki Mohammed na VI, inda za su yi shawarwari kan bunƙasa hulɗoɗin tattalin arziki a fannonin samad da makamashi, da ayyukan ban ruwa, da yawon shaƙatawa da kuma kimiyya da fasaha. Za su kuma tattauna batutuwan da suka shafi harkokin Gabas Ta Tsakiya da yaƙi da ta’addanci.

Da can dai, Rasha, ita ce ta fi sayar wa Marokko man fetur. Amma alƙaluman baya-bayan nan da aka buga na nuna cewa ƙasar Saudiyya da kuma Iran, sun sha gaban Rashan, inda a halin yanzu take jeri na 3 a sahun kasashen da Marokkon ta fi cinikin man fetur da su.