Shugaba Obama na ziyara a Burma
November 19, 2012Ziyarar ta shugaba Obama ita ce ta irinta ta farko da wani shugaban Amurka da ke an gadon mulki ya kai ƙasar ta Myanmar, inda ake sa ran zai gudanar da jawabai musamman game da batutuwan da su ka dangancin yunƙurin mahukuntan na wannan lokacin na girka tsarin demokraɗiyya da kuma zaburar da su wajen gudanar da gyare-gyare na siyasa.
Tuni dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bani adama su ka fara sukar ziyarar ta shugaba Obama saboda a cewarsu hakan nuna cikakken amincewa ne da gwamnatin ta Myanmar duk kuwa da cewar ba su kammala gudanar da gyara ga tsarin demokraɗiyyar ƙasar ba, to sai dai Obaman ya ce ba wai amincewarsa da gwamnatin ya ke son nuna ba, ya na son nuna cewar an samu sauye-sauyen demokradiyya a ƙasar ne.
Gabannin ziyarar ta sa dai, gwamnatin ta Myanmar ko Burma ta yi shelar yin afuwa ga wasu fursunonin sama da sittin wanda su ka haɗa da wasu fitattun 'yan siyasar ƙasar da a baya ake tsare da su.
Mawalafi : Ahmed Salisu
Edita : Muhammad Nasir Awal