1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Kim da Moon za su gana

Abdul-raheem Hassan
September 16, 2018

Tawagar jami'an gwamnatin Koriya ta Kudu, tare da dandazon 'yan jaridu sun nufi Koriya ta Arewa domin halartar taron koli karo na uku tsakanin shugabannin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/34w2T
Kim Jong Un und Moon Jae In
Hoto: picture-alliance/dpa/Korea Summit press

Tuni hukumomin Koriya ta Arewa suka shirya tarbar tawagar Shugaba Moon Jae-in mai kawatarwa a babban filin sauka da tashin jiragen sama a birnin Pyongyang, dan halartar taron koli kan makamin nukiliya da takorarsa Kim Jung-un da aka shirya a ranar Talatar da ke tafe.

Wannan dai shi ne karo na uku da shugabannin za su gana da juna cikin shekarar 2018, sai dai sun gana a watan Afirilun da ta gabata a wani kauyen da ke kan iyakar kasashen biyu.

Ana sa ran ganawar za ta yi tasiri wajen inganta dangantaka tsakanin Koriyoyin biyu, bayan daukar tsawon lokaci ba a ga maciji da juna.