1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Jonathan yayi alkawarin shawo kan matsalar ta'addanci a Najeriya

August 27, 2011

Shugaban ya yi wannan furuci ne dai a daidai lokacin da ƙungiyar tuntuɓar Juna ta Dottijan arewacin Nigeria, ta yi Allah wadan harin Bom da aka kai harabar Majalisar Ɗunkin Duniya a ranar Juma'a, da ya kashe mutane 18

https://p.dw.com/p/12OgV
Goodluck JonathanHoto: AP
A ranar Asabar ne dai shugaba Goodluck Ebele Jonathan na Najeriya ya kai ziyarar gani da Ido a harabar Majalisar Ɗunkin Duniya da aka kai hari a ranar juma'a. Ita kuwa ƙungiyar tayi wannan furuci ne a wata takardar da  Anthony Sani da ke zama kakakinta ya gabatarwa  manema labarai. Sun dai bayyana rashin jin daɗinsu dangane da fashewar wani Bomb a offishin Majalisar Ɗunkin Duniya da ke a Abuja, wanda ya lashe rayukan jama'a da yawar gaske da kuma raunata sama da 50
cikin su kuwa har da fararen fata.

Ƙungiyar ACF tare da sauran ƙungiyoyin dake fafatukar ci-gaban arewa sun bayyana cewa wannan al'amari dai ya tayar da hankalin hukumomin ƙasar dangane da irin cin mutunci tare da zubar da darajar Nigeria a Idanun ƙasashen ketare da waɗannan suka kai wannan hari.
Bugu da ƙari ƙungiyar ta  ACF ta nuna rashin jin daɗin ta kan ƙaruwar tarwatsewar miyagun makamai a jihohin arewa , wanda  ke bukatar ganin an gaggauta ɓullo da hanyoyin warware ƙaruwar wannan bala'in.


Mawallafi: Ibrahima yakubu

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar