Shugaba Jonathan ya gabatar da kasafin kuɗi
October 10, 2012Bayan share tsawon lokaci ana kai kawo shugaban Najeriya ya mika sabon kasafin kasar na shekara mai zuwa a gaban wani zaman hadin gwiwa na majalisun kasar biyu a Abuja
Kasafin na Naira milliyan zambar dubu huɗu da milliyan dubu ɗari tara, na zaman ƙarin kashi biyar cikin dari na dan uwansu a shekara mai karewa.
A wani jawabin da ya yi wa zaman majalisun kasar biyu na hadin gwiwa dai, shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan dai yace a badin kasar za ta kashe tsabar kudi har tirilliyan ɗaya da milliyan dubu 540 domin manyan ayyuka a yayin da kuma harkokin na yau da kullum za su lashe tirilliyan biyu da milliyan dubu 410.
An dai gina kasafin kudin kasar ne bisa ma'aunan da suka hada da samar da akalla gangar mai milliyan biyu da dubu 530 a kullu yaumin tare kuma da sai da ita a kalla dala 75 a kasuwanni mai na kasa da kasa.
Harkar ilimi ce dai ta tashi da kaso mafi tsoka na Naira milliyan dubu 426 sai kuma ma'aikatar tsaro mai billiyan 349. Yan sandan kasar ta Najeriya da ke da alhakin tsaro da kuma ke ci gaba da fuskantar jerin kalubalen tsaron ma dai za su dara domin samun kasafin da ya kai Naira milliyan dubu 319, a wani abun da shugaban kasar ya kira kudurin san a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a daukacin kasar, inda yace.
"Muna sane da tasirin kalubalen rashin tsaro ga kasar mu, kuma mun dauri aniyar tabbatar da kawo karshen sa. Ina mika ta'azziya ta ga yan kasar mu da suka rasa masoya a kisan kwanan na garin Mubi dama yan uwansa a sassa daban daban na kasar nan"
Tuni mun yi kame a Mubi kuma ina tabbatar wa yan Najeriya cewar duk masu ruwa da tsaki to za su fuskanci fushin sharia.
To sai dai kuma in har yanzu tana da baki da duhu ga batun na tsaro dai hankalin alummar kasar a tunanin shugaban ya kamata ya kwanta sakamakon karuwar tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a yanzu haka.
Kazalika tun ba'a kai ko ina ba alamun ci gaban rikicin da ya kai ga dage gabatar da kasafin da kusan mako gudu ya fara kunno kai sakamakon matakin yan majalisar wakilan kasar na daga kiyasin kudin man daga dala 75 kan kowace gangar ya zuwa dala 80
Yan majalisar da suka dau hutun sati guda suka kuma zagaya daukacin mazabun kasar dai sun shaida wa shugaban cewar, ikirarin ci gaban na isa bai isa karkara dama biranen da a cewar shugaban majalisar wakilan kasar Aminu Waziri Tambuwal ke cikin halin ni yasu ba
"Mune wakilan mutane kuma a matsayin mu na wakilan mutane mun san yanda al'amura suka lalace. Dole ne saboda haka mu yi aiki tare domin ceto kasar mu daga tsananin talauci"
Shi cigaban da ake Magana dole ne ya isa ga duk yan Nigeria ba ya tsaya ga masu rike da mukaman gwamanati ko kuma wadanda suka samu yar dama kan ragowar al'umma ba.
An dai sha yan kallo a tsakanin majalisar da bangaren zartarwa ga kokarin aiwatar da kasafin kasar na shekara mai karewa, rikicin kuma daga dukkan alamu bai nuna alamar karewa ga Najeriya da kai ke rabe tsakanin gwamnatin dake bin addinin jari huja da kuma majalisun dake son gani a kasa.
Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Usman Shehu Usman