Shugaba Buhari zai sake tsayawa takara
April 9, 2018Labarin ya fito ne a daidai lokacin da 'ya'yan jam'iyyar suka shirya wani taro da nufin rikici a tsakanin juna to sai dai kuma sun buge da tsallen murna a banagre na 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki da babu zato ba kuma tsammani suka samu labarin takara ta shugaban kasar. Duk da cewar dai zuciyarsu tafi karkata ga neman mafitar rikicin zarcewa ko kuma karewar mulkin shugabannin jam'iyyar a matakai daban-daban, shigar sauri ta Buharin da ya sanar da takarar ta shi dai ta faranta ran kusan dukkanin 'ya'yan jam'iyyar da suka manta da batun rikici suka kuma fada a cikin murna.
Babban kalubalen da ke gaban jam'iyyar ta APC dai na zaman shiga zaben a cikin halin rabuwa. To sai dai kuma a fadar Senata Abu Ibrahim da ke zaman dan majalisar dattawa daga Katsina takarar ta Buhari na shirin kawo sauyi a cikin jam'iyyar da a baya ta nuna alamun tangal-tangal. Sai dai da ta kai ga reshen jam'iyyar a jihar kano barazanar kai kara ta shugaban kasar in har bai fito ya nuna shawarar sake takarar mai tasiri ba.
Har wa yau jam'iyyar kuma a fadar Senata Ahmed Lawal da ke zaman shugaban masu rinjayen APC a cikin majalisar dattawa ta kasar ta amince ya zuwa zabe tare da bada damar sake takara ga shugabannin yanzu a matakai daban-daban. Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba ga masu tsintsiyar dake shirin komawa filin daga amma kuma a cikin halin dar-dar.