Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2021
October 8, 2020Talla
Shugaban Najeriya Mohd Buhari ya gabatar wa majalisun dokokin kasar kasafin kudin shekarar 2021 a dai-dai loakcin da kasar ke fuskantar koma bayan tattalin arziki.
Shugaban ya gabatar da kasafin da ya kai naira triliyon 13.1, wanda ya zarta kasafin kudin bara da kashi 20 cikin dari. Shugaba Buhari ya ce kasafin kudin bana zai taimaka wa farfado da tattalin arzikin kasar.
Annobar Corona da rashin samun kudaden shiga da faduwar farashin danyen man fetur a duniya na daga cikin manyan matsaloli da suka nakasa tattalin arzikin Najeriya.