Shugaban Yemen ya koma gida daga Saudiyya
September 22, 2015Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Aden na ƙasar Yemen a karon farko tun bayan da ya yi kaura zuwa Saudiyya bayan da ƙasar ta shiga yanayi na yaƙi da mayakan Houthi.A wani labarin kuma wani ruwan bama-bamai da kasar Saudiyya ta jagoranta a yankunan da al'umma ke zama a ƙasar Yemen a ranar Talatan nan ya yi sanadin hallaka mutane 21 ciki kuwa har da fararen hula kamar yadda shedu da jami'an lafiya suka tabbatar.
Wannan farmaki dai an kai shi ne da nufin farwa wasu 'yan Houthi da ke samun goyon bayan kasar Iran a yankin Sabeen da ke makwabtaka da birnin na Sanaa sai dai gidaje da ke kusa da yankin da ke zama na fararen hula suma abin ya shafesu.A jiya Litinin ne dai mayaƙan na Houthi suka yi bikin murna na cika shekara daya da kwace iko da birnin na Sanaa bayan samun goyon bayan dakarun da ke biyayya ga tsohon shugaban ƙasa Ali Abdullah Saleh.