A cikin shirin za a ji cewa, a kasar Iraki, a yayin da ake ci gaba da kidayan kuri'u a zaben majalisar dokoki da ya gudana a wannan Asabar, mutane akalla uku aka tabbatar da mutuwarsu a sanadiyar tashin wani bam a yankin Kirkuk, sannan Koriya ta Arewa ta tsayar da ranakun lalata makaman ta na nukiliya.