Wani rahoto da wasu kwararru na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar, ya nunar cewa daga watan Janairu zuwa Satumba na 2017 Koriya ta Arewa ta samu kudadan shiga da suka kai dalla miliyan 200 na kayayakin da take fitarwa, duk kuwa da hanin da aka yi mata sakamakon takunkumin da ke kanta.