Bayan labaran duniya a cikin shirin za a ji cewa Taliban da ta kwace mulkin kasar Afghanistan ta ce ba za ta laminci noma da siyar da Opium ba. Sai dai halin yunwa da jama'a ke ciki ka iya assasa noma da cinikin ganyen a kasar da ke samar da akalla kashi 80 cikin dari na opium a duniya.