A cikin shirin za ku ji yadda Shugaban kotun kasa da kasa mai hukunta wadanda suka aikata miyagun laifuffukan yaki ya musanta kallon kotun da ake a matsayin wacce ke tuhumar shugabannin kasashen Afrika kadai, yayin wata ziyarar kokarin kyautata danganatakar kotun da ma fahimtar aiyyukanta daya kai a Najeriya inda ya gana da ministan kula da harkokin kasashen wajen kasar.