1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wasanni: Gasar kofin kwallon kafar duniya

Suleiman Babayo LMJ
December 26, 2022

Bayan kammala wasan neman cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar Ajentina ta zama zakara, yanzu hankali ya fara komawa kan kasashe uku da za su dauki nauyin gasar ta gaba.

https://p.dw.com/p/4LR8y
FIFA | Amirka | Kanada | Mexiko | Kwallon Kafa | 2026
Kasashen Amirka da Kanada da Mexiko, za su karbi bakuncin kwallon kafa a 2026Hoto: Getty Images/AFP/K. Kudryavtsev

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA, ta bayyana cewa ta shirya ganin kasashe 48 sun halarci gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekara ta 2026 da kasashen Amirka da Kanada da kuma Mexiko za su shirya. Hukumar ta samu nasara kan shirya gasar da aka kammala fiye da mako guda a kasar Katar, inda Ajentina ta zama zakara bayan samun nasara a wasan karshe a kan Faransa. Kasashe 32 ne suka halarci gasar da aka kammala, kuma mayar da gasar zuwa kasashe 48 ya nuna irin gagarumin sauyi na yawan kasashen da za su halarci gasar ta gaba.

FIFA | Amirka da Kanada da Mexiko | Kwallon Kafa | 2026
Kwallon Kafa 2026 a kasashen Amirka da Kanada da Mexiko Hoto: Getty Images/AFP/M. Antonov

An fara gasar neman cin kofin kwallon kafa ta duniya a shekarar 1930 fiye da shekaru 90 ke nan, inda aka fara da kasashe 13 sannan aka mayar zuwa kasashe 16 a 1934 zuwa 1978, kana aka kara zuwa kasashe 24 da suka halarci gasar cin kofin kwallon kafar ta duniya a shekarar 1982. Wannan karin zuwa kasashe 48 da shugaban hukumar na yanzu Gianni Infantino ya bullo da shi, kasashen Afirka da na Asiya za su fi amfana da shi sakamakon yawan kasashen nahiyoyin da za a kara. Ganin cewa kasashe uku da za su shirya gasar Amirka da Canada gami da Mexiko sun kasance na gaba-gaba a duniya wajen girman kasa, kuma Amirka ke jagorancin ci-gaba na zamani a fannoni dabam-dabam a duniya.
Kasar Aljeriya ta mika takardar neman daukar nauyin gasar neman cin kofin kwallon kafar kasashen Afirka ta 2025, ga hukumar kula da wasan kwallon kafar nahiyar. Hakan na zuwa  ne sakamakon kwace damar daga kasar Guinea, saboda rashin ingantattun wuraren da za a gudanar da wasannin. Tuni kasar Maroko mai makwabtaka da Aljeriyan kana abokiyar hamayyarta, ita ma ta mika takardar neman karbar bakuncin gasar kamar yadda kasashen Najeriya da Jamhuriyar Benin ma suka mika bukatar ta hadin gwiwa domin daukar nauyin gasar.

Aljeriya | AFCON | Gasa | Maroko | Takara
Aljeriya na son karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta AfirkaHoto: MOHAMED ABD EL GHANY/REUTERS
Kenya | Mark Otieno Odhiambo | Hukunci
Dan tseren kasar Kenya zai fuskanci hukunci kan shan kwayoyin kara kuzariHoto: Olaf Rellisch/imago images

Hukumar tabbatar da da'a a fannin wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta dakatar da Mark Otieno dan gudun kasar Kenya daga wasa na tsawon shekara biyu, sakamakon karya dokokin amfani da kwayoyi masu kara kuzari. Gwajin da aka yi wa dan wasan ya nuna ya sha kwayar kara kuzari gabanin gudun mita 100 da zai halarta lokacin wasannin Olympic a birnin Tokyo na kasar Japan a watan Yulin shekara ta 2021. An yankewa dan wasan gudun Mark Otieno daga kasar Kenya mai shekara 29 da haihuwa hukuncin dakatarwa shekaru biyu, wanda ya fara daga lokacin da aka kama shi ya aikata laifin a shekara ta 2021.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani