Shirin kara harajin kiran waya
August 8, 2022A yayin da ake ci gaba da fuskantar barazanar karyewa tattalin arziki, gwamnatin tarrayar Najeriya ta zaiyana sabon shiri na kara jerin harajida nufin kaucewa rikicin man fetur da ya bar kasar cikin rudani.
Kama daga ita kanta tarraya ya zuwa ga jihohi, rikicin rashin kudin ya yi nisa kuma na tasiri ga kokari na sauke nauyin miliyoyin al'ummar kasar a halin yanzu. Duk da tarihi na farashin man fetur, yawan man da kasar take haka a yanzu, ya ragu da kusan kaso arba'in cikin dari a sakamakon annobar fasa bututu da satar man zuwa kasashen waje.
Amma kuma Abujar na neman sauyin taku tare da bullo da wasu jeri na matakai da watakila kara haraji da nufin tunkarar rikicin da ko bayan aiyuka na raya kasa ke barazana ga makomar ma'aikata a jihohin kasar dabam-dabam. Abujar alal misali, ta sanar da wani sabo na haraji na waya ta salula da yake shirin fara aiki a badi, kuma ke neman ninka farashin na waya da kusan kashi dari.
Maimakon Naira ashirin kan kowane minti, sabo na harajin ya tanadi kara kudin kiran ya zuwa Naira arba'in kan kowane minti. Ko bayan nan, Abujar ta kuma ce, tana nazarin kara haraji na mai saye daga kaso 7.5 cikin dari ya zuwa kasji ashirin.
Sababbi na matakan na zuwa ne kasa da 'yan sa'o'i da shawarar gwamnoni na jihohin da ke fadin akwai bukata ta sallamar ma'aikatan da suka zarta shekaru hamsin da haihuwa da nufin rage kudade na batarwa da ke ta hauhawa a halin yanzu. Gwamnatin na a tsakanin sauyin takun kashe kudi, da nufin tsira daga cikin barazanar rushewa, ko kuma ci gaba a cikin karatun al'ada a cikin yanayi maras tabbas.
Gwamnatin Najeriyar na shirin kare shekara tare da gibin da ya kai kusan kashi arba'in cikin dari na kudade na shigar da take da bukata da nufin sauke nauyin da ke tsakaninta da talakawan kasar.