Bukukuwan Kirsimeti sun kankama a Afirka
December 24, 2019Al'ummar Kiristoci a kasashen Afirka da dama na gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara. Sai dai a daidai lokacin da a jamhuriyar Nijar Kiristocin ke kawata mujami'u da sayen kayan yin kyaututtuka ga jama'a, a Najeriya masana ne suka fara gargadin jama'a a game da yiwuwar fuskantar hare-haren Boko Haram a wasu yankunan kasar a lokuttan bukukuwan.
Mujami'u a birnin Zinder na Jamhuriyar Nijar, sun sha kwalliya, a yayin da mabiya addinin na Kirista suke ci gaba da gudanar da sayen kayayyakin kyautar da suke yi wa yara a wannan lokaci. Sai dai bikin Kirsimetin na bana ya zo ne kwanaki kalilan bayan da 'yan ta'adda suka halaka sojojin Nijar 71 a wani kazamin hari da suka kai masu a garin Inates na kan iya da Mali. Wannan ce ta sanya Mujami'u da dama suka tsara gudanar da addu'o'i na musamman na neman ramahama ga mamatan da kuma neman Allah ya kare kasar Nijar da tabbatar da zaman lafiya a cikinta.
A Najeriya kuma shirye-shiryen bukukuwan na Kirsimeti na gudana ne a cikin yanayin zaman dar-dar na fargabar yiwuwar fuskantar hare-hare daga mayakan Kungiyar Boko Haram kamar yadda ta kasance a shekarun baya. A kan haka ne mahukunta ke ta gargadin jam'a kan su yi taka tsan-tsan da kuma bai wa jami'an tsaro hadin kai a aikinsu na tabbatar da tsaro musamman a cikin Jihar Borno.
A kasar Kamaru kuma al'ummar yankin masu magana da Turancin Inglishi na suma gudanar da shirye-shiryen bukukuwan na Kirsimeti da sabuwar shekara a cikin halin na rashin tabbas a sakamakon tarbarewar harakokin tsaro da ke da nasaba da rikicin 'yan awaren yakin.
A kasar Togo kuma sakamakon yawautar haduran ababen hawa a wannan shekara, gwamnatin wannan kasa ta yammacin Afirka ta aiwatar da shirin gwajin barasa a cikin jini. Ma'aikatar tsaro da walwalar jama'a ta ce wannan gwajin da ya zo gabanin bukuwan kirisimeti da sabuwar shekara ya wajaba a kan duk direbobin, kama daga na babur har ya zuwa kanana da manyan motoci. Gwamnatin kasar ta Togo ta dauki wannan mataki ne a matsayin rigakafin afkuwar hadurran da ake yawan samu musamman a lokuttan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.