Shekaru biyu da fara yakin Yemen
March 27, 2017Asusun na UNICEF ya bayyana hakan ne a dai-dai lokacin da ake cika shekaru biyu cif, da fara kai hare-haren taron dangi na kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiya a Yemen din, wanda ya haddasa matsalar rashin abinci mai gina jiki, da aka kiyasta yara akalla 462.000 na cikin halin tsaka mai wuya na yunwa da rashin ingantaccen abinci a sassa daban-daban na kasar. Sai dai a hannu guda mahukuntan Yemen din na gudanar da shagulgula na cika shekaru biyu da fara hare-haren na Saudiya da kawayenta. A jawabin da ya yi yayin da suke shagalin cika shekaru biyu na wannan gumurzu, Hadi Adnan Alkaf mataimakin gwamnan birnin Aden da ke hannun gwamnatin Shugaba Abedrabbo Mansour yaba wa ya yi da irin taimakon da suke samu daga Saudiyan da kawayenta yana mai cewa:
"Muna yin shagali domin nuna godiyarmu ga rundunar taron dangi da suka kawo dauki ga Shugaba Abedrabbo Mansour Hadi domin taimakonsa ya yaki 'yan tawayen Houthi da kuma magoya bayan tsohon Shugaba Ali Abdullah Saleh."