1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da sansanin gwale gwale na Nazi a Auschwitz

Abdullahi Tanko Bala
January 26, 2020

Shugabannin kasashen duniya da mutanen da suka tsira daga sansanin gwale gwale na Auschwitz su kimanin 200 za su halarci bikin tunawa da ranar da aka 'yantar da sansanin wanda ya zama tarkon mutuwa a wancan zamani.

https://p.dw.com/p/3Wq9N
Polen, Oswiecim:  Konzentrationslager Auschwitz
Hoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

Shekaru 75 kenan cif da sojojin Rasha suka 'yantar da sansanin gwale gwale na 'yan Nazi da ke Auschwitz a kudancin Poland. A ranar 27 ga watan janairu na kowace shekara akan yi bikin tunawa da wannan rana domin yin waiwaye kan azabtarwar da aka yiwa a Yahudawa a sansanin na Auschwitz. Mutane kimanin miliyan daya yawancin su Yahudawa gwamnatin Nazi ta Hitler ta kashe a sansanin a lokacin yakin duniya na biyu.  

Sai dai yawancin mutanen da aka kai sansanin a jiragen kasa cikin taragun shanu basu kai labari ba. Daga tashar jirgin kasa aka wuce da su kai tsaye zuwa inda aka tube su aka tura su cikin wani zaure mai cike da iska mai guba ta Cyclon B aka kone su kurumus aka kuma shekar da tokar.

Sansanin gwale gwale na Nazi a Auschwitz
Sansanin gwale gwale na Nazi a AuschwitzHoto: picture-alliance/dpa/J. Woitas

Katrina wata matashiya ce malamar makaranta daga birnin Dresden. Ta ce shiga zauren mai bakin duhu da shakewa inda wani bututu ke fidda bakin hayaki waje abin tashin hankali ne matuka a rayuwarta.

“Ta ce babu shakka an fuskanci wani yanayi na tashin hankali, musamman idan ka bude ido ka ganka a tashar karshe, idan ka ga yadda ake kashe mutane, ka ga bakin hayaki na tashi daga rufin gini, a sannan za ka tabbatar da cewa an kone mutane kurumus. Kuma babban takaici shine 'yan Adam suka aikata wannan ba wasu aljanu ba."

Ziyarar shugabanni sansanin Auschwitz
Ziyarar shugabanni sansanin AuschwitzHoto: Getty Images/AFP/B. Siedlik

Wani bangare na wurin tarihin ya maida hankali ne kan akidun 'yan Nazi. Yana dauke da faya fayen majigi na jawaban kiyayya da kyamar Yahudawa daga manyan jami'an Nazi da kuma kiraye kirayen da suke yi da suka yi wa lakabi da mafitar karshe ta Yahudawa. Pawel Sawicki jami'in yada labarai ne a gidan adana tarihin na Auschwitz. Yace akwai bukatar maziyarta da ke zuwa sansanin su dauki darasi daga tarihin Nazi na Jamusa zamanin baya domin yin taka tsantsan da wadannan akidoji.
“Yace ya kamata mu samo hanyar da za mu yi magana kan gaskiyar abubuwan da suka faru na tarihi a wannan mummunan wuri da zai iya cusa wa wani ra'ayi ko karfafa masa gwiwa. Mu duba hanyoyin tattauna tasirin da wannan lamari ya yi ga rayuwar mu a yau. A wurare da dama a duniya, a yau muna ganin tasirin akidun kiyayya. A wurare da dama ana mayar da mutane tamkar tabbobi, akidar kisan kare dangi na karuwa. Matakin kare dangi bai fara da kisa ba, yawanci yana faruwa ne da akida. 

Wadanda suka kai ziyarar sun amince cewa wuri ne da ya kamata kowane mutum ya ziyarta musamman a lokacin da galibin wadanda suka tsira daga sansanin suke da shekaru 90 a duniya. Idan suka kaura zai rage ga 'yan baya su bada labarin sansanin na Auschwitz domin tabbatar da cewa irin wannan bala'i bai sake faruwa ba.