Tuni da ranar da aka sace 'yan matan Chibok
April 14, 2021A Najeriya a yau ake tuni da cika Shekaru 7 da sace 'yan matan Sakandaren garin Chibok da mayakan Kungiyar Boko Haram suka yi a ranar sha hudu ga watan Afrilun 2014. A wancan lokacin dai, gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa, dalibai kimanin 276, 'yan shekaru tsakanin 12 zuwa 17 aka sace daga makarantar da ke jihar Borno inda mayakan suka hana zaman lafiya. Wasu daga cikin daliban sun kubuta wasu kuma gwamnati ta 'yanto su, sai dai kawo yanzu akwai wasu fiye da dari da ke hannunsu kamar yadda Kungiyar Amnesty International ta tabbatar. A gangamin neman ganin an kubuto su aka samar da Kungiyar Bring Back our Girls.
Tun bayan sace 'yan matan na Chibok, kasar ta ci gaba da fuskantar barazanar tsaro daga mayakan dama wasu karin 'yan bindiga da suma suka shiga aikin sace dalibai daga makarantun kwana don neman kudin fansa, tun daga watan Disambar bara, an kai hare-hare sau biyar a makarantun kwana. A yayin da aka 'yanto da dama daga cikin wadanda aka sacen, har yanzu akwai wadanda ke hannun 'yan bindiga. Wannan ya janyo nakasu ga ilimi inda ake rufe makarantun kwana a yankunan da ake fargabar aiyukan 'yan bindigan. Unicef ta ce yara masu kananan shekaru sama da miliyan goma, ba sa zuwa makaranta a Najeriya.