1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 25 da kisan kare dangi a Ruwanda

April 6, 2019

Akalla mutane dubu 800 suka hallaka a rikicin na Tutsi da Hutu, har yanzu Ruwanda ta kasa murmurewa daga batun kabilanci. Sai dai a baya bayan nan gwamnati ta bullo da sabbin dubaru na sulhunta kabilun kasar.

https://p.dw.com/p/3GPFj
Ruanda Gedenkstätte an Völkermord in Nyamata
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Batun na kashin kiyashin da ya auku tsakanin 'yan kabilar Tusi da Hutu a kasar Ruwanda na a matsayin irinsa na farko a tarihi da ya auku a nahiyar Afirka kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.

Duk da yake rikcin a yanzu ya shafe tsawon shekaru 25,  galibin shari'o'in kasar da ma wasu hanyoyin da ake dauka a yanzu na fatan ganin an samu sulhu ne tsakanin kabilun baya ga amincewa da yadda aka aikata laifi.

A yankin Rusizi da ke yammacin kasar Ruwanda a tsaunukan Mushaka, Nicolas dattijo ne dan shekaru 45 da ya dandani zama na gidan wakafi bayan ya kashe mahaifin wata matashiya da yanzu take da shekaru 43 mai suna Marianne a yayin tashin hankalin, wanda hakan ke a matsayin wasu alamomin nuna cewar an kama hanyar sulhunta rashin jituwa a tsakanin kabilun kasar. Nicolas ya ce:

"Kaico a lokacin kafin fadawa a rikicin kabilancin ni wani salihi ne cikakken mabiyi addinin kirista, to amma wub da rikicin ya soma muka yi tatattaki har zuwa gidan Jean Sumba kuma muka hallakashi. Na fuskanci zuwa gidan kaso saboda hakan kana kuma bayan na kammala a wani tsarin da coci ta bullo da shi na neman gafara na je har gidan su Marianne na tambayi gafarar danginta kuma na bayyana masu da cewar shedan ne mafari."

Cibiyar tunawa da kisan kare dangi a birnin Kigali
Cibiyar tunawa da kisan kare dangi a birnin KigaliHoto: DW/I. Mugabi

Marianne dai da ta rasa mahaifinta tun tana budurwa ta san sarai abin da ya faru game da mutuwar babanta, ta kuma san da cewar Nicolas ne tsohon makwabcin da ya yi zama a gidansu, inda ta ce.

"Da a ce wannan tsarin na yin afuwa daga dangi da 'yan uwan mamata bai shigo ba da har yanzu Dattijo Nicolas na kargame a gidan yari, mun bukaci da ya bayyana a gabanmu ya nemi gafara kuma mun gafarta mai."

A yanzu dai suna da dama wadanda suka ci moriyar irin wannan afuwar ta hanyar wannan sabon tsarin da gwamnatin kasar Ruwanda ta bullo da shi, inda ake tilasta wa mutanen da su kai kansu gidan wadanda suka kashe don neman yarda, amma wasu 'yan kasar na cewa da gwamnatin Ruwanda kamata ya yi ta rinka yin adalci tsakanin kabilun kasar ba tare da nuna fifiko daga wata kabila kan wata kabilar ba.

Tun a shekarar 2015 kwamitin sulhunta 'yan kasar ke wallafa bayanan cewar kashi 92 cikin 100 na 'yan kasar sun yafe wa juna duk da yake ana fama da matsalolin rashin jituwa tsakanin kablun biyu a kasar. Gwamnati na ci gaba da amfani da alkaluman kamar yadda Fidèle Ndayisaba, babban sakataren hukumar yake cewa.

"Wannan ma'auni na hadin kan 'yan kasa na fuskantar 'yar tangarda saboda har yanzu da akwai wasu 'yan kasar da ke nuna alamomin masu nasaba da kabilanci da ma kisan kiyashin. Har yanzu da akwai wasu sauran jama'a da ba su taka kara suka karya ba da ke da wannan manufofin."

'Yan Ruwanda ke bukukwan na tunawa da rikicin Tutsi da Hutu da ya auku shekaru 25 kenan, yayin da a share daya ita kuwa gwamnatin kasar na kargame duk wani wanda ta lura yana neman sake zazafa batun.