Shari'ar masu kyamar baki a Jamus
August 7, 2013Wata kotu a birnin Munich da ke nan Jamus, wadda ke sauraren shari'ar mutane hudu da ake zargi da tallafawa masu akidar 'yan Nazi, wadanda ke kyamar baki, a irin ta'asar da suka tafka, a yanzu ta dage ci gaba da sauraren shari'ar - har sai bayan makonni hudu, wato a ranar biyar ga watan Satumba dake tafe. Shari'ar dai ta shafi kissan wasu Turkawa tara ne da wasu 'yan kasar Girka, game da wata 'yar sandar Jamus a laifuffukan da a ka aikata cikin tsukin shekaru 10. Dage sauraren ka'rar dai, ya zo ne bayan sauraren shaidu 90, yayin da kotun kuma ke fatan sauraren karin shaidu 500.
Wakiliyar DW, Michaela Küfner ta yi karin haske a kan shari'ar:
Ta ce " Shari'ar dai ta kunshi irin rawar da jami'a 'yan sanda suka taka, da gazawar hukumomi na yin anfani da bayanan da suka samu game da ta'asar a kan lokaci."
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu