1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamus na cikin tsaka mai wuya.

Pohl Ines Kommentarbild App
Ines Pohl
June 2, 2019

Sakamkon zaben 'yan majalisar dokokin Tarayyar Turai da ya gudana mako guda, a yanzu ya jawo mummunar girgiza a siyasar kasar Jamus, biyo sanarwar yin murabus da shugabar jam'iyar SPD Andrea Nahles.

https://p.dw.com/p/3JdBU
Deutschland Bundestag in Berlin | Haushaltsdebatte | Seehofer & Scholz & Merkel
Hoto: picture-alliance/dpa/K. Nietfeld

Lamarin dai ya wuce iya siyasar cikin gidan jam'iyar Andrea Nahles kawai, amma matsala ce da za ta kai ga barazana ga kawancen SPD da CDU. A yanzu dai dukkan jam'iyyun biyu wadanda sune jam'iyyu da suka fi girma a kasar Jamus, kuma su ne ke ta kafa gwamnati a siyasar kasar, suna cikin tsaka mai wuya, inda kusan ko wane zabe farin jininsu ke kara dusashewa. 

Mummunar alama ga sabuwar jagorar CDU

A gaba kuma sai CDU: Tun lokacin da Angela Merkel ta sauka daga jagorancin jam'iyarta, a duk lokacin da aka gudanar da zabe walau na jihohi ko na kananan hukumomi, jam'iyyar sai kara rasa madafun iko ta ke yi. Sabuwar shugabar jam'iyyar wace ke kan turbar maye gurbin Angela Merkel, tun zuwanta sai al'amura suke kara zamo mata mai farar kafa. Annegret Kramp-Karrenbauer, ko da a zaben 'yan majalisar dokokin Tarayyar Turai ba wani abun kirki da jam'iyyar ta yi, sai ma akasi aka samu. Ga kuma illar rashin iya magana, inda kalaman da ta yi na sukar wani mai mu'amala da shafin Youtube. Wannan sukar da ta yi bai tsaya ga mutuncin Kramp-Karrenbauer ba, amma dukkan jam'iyar ya yi wa illa.  

SPD na neman matsayinta

Deutschland Berlin Scheidemannbalkon | Steinmeier & Schäuble
Hoto: picture-alliance/dpa/Sandra Steins/BPA

Ga jam'iyar SPD matsalar ta fi sarkakiya.  Tun shekaru shida da suka gabata jam'iyar ita ce ke yin kawance da gwamnati mai mulki, to amma kokarinsu bai taba yin tasirin rage farin jinin shugabar gwamnatin Jamus ba. A takaice ma dai dukkan kyawawan tsare-tsare da sauye-sauyen da SPD suka samar cikin gwamnatin, duk Merkel ce ta kwashe ladan abin da suka yi, don ita ake yabawa maimakon jam'iyar SPD. Kasancewar duk tsarin kamar na iyali da albashin ma'aikata da SPD suka amma samar Merkel ce ke samun yabo, hakan ya sa SPD bata samun komai illa yawan sauya shugabannin kawai. 

A yanzu shugabar jam'iyar SPD ta sanar da yin murabus, hakan na nufin komai ya kawo iya wuya, don haka jam'iyar kan iya ficewa daga gwamnatin hadaka, koma me zai iya faruwa sai ya faru. 

Ines Pohl Kommentarbild App
Ines Pohl , Babbar editar DWHoto: DW/P. Böll

Kada a yi saurin zare takwabi

Wannan matakin na da hatsari. Idan haka ta kai ga dole a sake zaben majalisar dokoki Tarayyar Jamus a bana shiri? Walau jam'iyar SPD ko kuma kawancen DCU da CSU babu dayansu da ta shirya tsarin zabe wanda zai iya gamsar da bukatun da 'yan kasar Jamus ke nema a yanzu. Batun kare mahalli na daga cikin bukatun a halin yanzu. Koma dai me ya faru demokradiya ta tabbata a Jamus, don haka duk ma abin da za'a yi, idan ma zabe aka sake jam'iyyar masu tsatsauran ra'a yi ba za ta kafa gwamnati ba. Wannan kuwa shi ne kyakkyawan labari a kasar Jamus, a daidai lokacin da siyasar ke cikin tsaka mai wuya. 

Rawar Jamus a duniya.

Jamus na da matsayi a siyasar duniya yanzu, don haka bai kamata rikicin shugabancin jam'iyyu ya sauya matsayinta ba, kamar abin da ka iya faruwa a kwanaki da ke tafe. SPD da CDU dukkansu ko wace bai kamata ta zare takwabinta ba, kamata ya yi su nemi mafita kwakkwara. A cikin karamin lokaci siyasar Jamus za ta dai-daita, kuma shi ne hasashen kawayenta na duniya. Mudddin dai shugabannin siyasar na tunanin gobe bai wai neman iko a yanzu ba.