1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhi: Duniya za ta fuskanci hatsari

May 11, 2018

Janyewar da Amirka ta yi daga yarjejeniyar nukiliya da Iran, ta kara jefa duniya cikin babban hatsari, ta kara sanya kokarin kwance damarar yaki cikin rashin tabbas.

https://p.dw.com/p/2xYhp
USA Donald Trump Ausstieg aus Atomabkommen mit dem Iran
Hoto: picture-alliance/abaca/D. Olivier

Tun gabanin daukar matakin janye Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran da shugaba Donald Trump ya yi, an yi ta rade-radin irin tasirin da wannan matakin zai yi. Yanzu dai bakin alkalami ya bushe kuma ma Trump baya ga janye daga yarjejeniyar ya kuma farfado da takunkuman karya tattalin arziki kan Iran da ma yin barazana kan duk wata kasa da ta yi hulda da kasar ta Iran.Tabbas wannan matakin ba zai sa duniya ta samu karin zaman lafiya ba. Hasali ma farashin hannun jarin kamfanonin kera makamai ya yi tashin gwauron zabi. Wani batun ma shi ne wannan mataki ba zai sa a samu saukin samun nasara a taron kolin da zai gudana da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ba.Trump ya bayar da hujjar cewa yarjejeniyar ba ta duba muradun tsaron Amirka ba, amma bai yi bayanin yadda ficewar za ta kare muradun tsaron Amirkar ba. Yarjejeniyar dai ta haramta wa Iran hanyoyin kera makaman nukiliya wanda kuma duniya ke sanya ido kai, matakin kuma da hana duk wani kokarin na tserereniyar makamai a yankin. Hatta sabon sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo bai nuna shakkun Iran na aiki da ka'idojin yarjejeniyar ba. Wani jami'in diplomasiyyar kasar Faransa ya ce Trump na da mastala da Iran ne amma ba da yarjejeniyar ba. Saboda haka duk tattaunawar da aka yi cikin watanni hudun da suka gabata tsakanin kasashen Turai da Amirka aka tsara rugujewarta duk da rangwamen da manyan kasashen Turan suka yi da kuma kokari na diplomasiyya hadi da ziyarce-ziyarcen Macron da Merkel da kuma Boris Johnson. Trump na kewaye ne da masu adawa da Iran. Baya ga sakataren harkokin waje Pompeo, akwai kuma sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaron kasa wato John Bolton, wanda a shekarr 2017 ya rubuta cewa burin Amirka shi ne ta kawo karshen juyin juya halin Islama na 1979 kafin a cika shekaru 40 da fara shi a Iran.A cikin hujjojin da ya bayar Trump ya dogara da wasu hotunan leken asiri da Firaministan Isra'ila Benjami Netanyahu ya nuna a makon da ya gabata, hotunan da bisa ga dukkan alamu na farfaganda ne, da ke zama wasu tsoffin hotuna da aka sake sarrafa su da ba su da wani muhimmanci da halin da ake ciki. Matakin da Trump ya dauka ya yi fatali da sakamakon tattaunawar da aka shafe shekaru 12 ana yi, ba tare da ya ba da wani zabi ba. Yanzu ana bukatar hadin kai da jajircewar kasashen Turai tare da Rasha da China su karfafa gwiwar Iran ta ci gaba da martaba ka'idojin yarjejeniyar.Hukumomin Iran za su kasance karkashin matsin lamba lamarin da watakila zai sa rikice-rikicen da ake yi a Yemen da Siriya da Lebanon da kuma Iraki su kara yin muni. Dole ne dai a sake duba tsarin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya da zai yi la'akari da muradu na halaliya ga dukkan wadanda batun ya shafa. Wannan ka iya zama hanya daya tilo ta samu sahihin zaman lafiya a yankin.

von Hein Matthias Kommentarbild App
von Hein Matthias wanda ya rubuta wannan sharhi wanda Mohammad Nasiru Awal ya fasara