An yi bikin sallah a Jamhuriyar Nijar
June 14, 2018Al'ummar jihar Agadez kamar sauran jihohi a Jamhuriyar Nijar, sun gudanar da bikin Sallah karama. Tun da sanyin safiya jama'a suka shirya domin zuwa Sallar Idi. Mai martaba sarkin Abzin Elhadji Oumaru Ibrahim Oumaru bayan sakonsa na barka da sallah zuwa ga al'ummar Agadez, ya yi fatan zaman lafiya ga kasa baki daya.
Batun koma bayan tattalin arziki a jihar Agadez bayan rufe wurin tonon zinariya mafi girma a jihar da gwamnatin Nijar ta yi da ma takaddama kan sana'ar safarar bakin haure sun kawo matsaloli masu yawa ga wasu iyalai da suka gagara samun kudin shiga don biyan wasu bukatu na su. Amman duk da haka wasu daga cikin al'ummar jihar ta Agadez sun baiyana farin cikinsu da ganin wannan rana bayan da suka kammala azumin na watan Ramadana lafiya.