Schumer: Netanyahu ne matsalar zaman lafiya
March 14, 2024Shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka Chuck Schumer ya yi kira ga Israila ta gudanar da sabon zabe yana mai cewa ya yi imani Firaminista Benjamin Netanyahu ya kauce hanya kuma ya zama cikas ga samun zaman lafiya a yankin.
"Ya ce mutum na hudu da ke zama tarnaki ga zaman lafiya a Israila shi ne Firaminista Benjamin Netanyahu wanda sau da dama ya na mika wuya ga bukatun masu tsattsauran ra'ayi a cikin ministocinsa kamar Smorteich da Ben-Gvir da kuma yan share wuri zauna da ke gabar yamma."
Shugaban masu rinjayen a majalisar dattijan ta Amurka ya ce masalaha kadai ita ce ta kasashe biyu da za su zauna daura da juna. Ya ce hakan shi ne zai kawo cigaba ga Israila da Falasdinawa.
Schumer shi ne Bayahude na farko mafi girman mukami a majalisar dattijan Amurka da ya yi kakkausar suka ga Netanyahu a jawabin da ya yi a zauren majalisar dattijan.