Schröder A Yemen
March 3, 2005A ziyarar ta Schröder ga kasar ta Yemen an shirya rattaba hannu akan wasu takardun yarjeniyoyin da suka shafi manufofin zuba jari da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Jamus da kasar Yemen. A baya ga haka akwai yiwuwar samun kwangila mai tsoka ga kamfanonin Jamus a kasar ta Yemen. Misali kamfanin Siemens na sa ran sa hannu akan wata takardar kwangilar da ta shafi Euro miliyan 130 akan sayarwa da kasar Yemen gangunan gas. Kazalika bisa ga dukkan alamu jami’an tsaron gabar tekun kasar zasu bukaci kwale-kwalen sintiri da yawansu zai kama tsabar kudi na Euro miliyan 80 daga wani kamfanin sarrafa jiragen ruwa dake garin Bremen. Kawo yanzun dai ba a cimma biyan bukata ba a game da fatan da aka yi cewar wannan ziyarar ta Schröder ga kasashen Lasrabawa zata share hanyar samun kwangila mai tsoka ga kamfanonin Jamus. A Saudiyya duka-duka kwangilar da aka samu ba ta zarce ta Euro miliyan 18 ba, a yayinda a can Bahrain kuma ba zato ba tsammni aka dage wa’adin rattaba hannu kan wata takardar kwangilar da ta shafi kudi Euro miliyan dubu daya domin gina wata masana’antar sarrafa magunguna. Ita dai Yemen janhuriya ce, bisa sabanin sauran kasashe shida na mashigin tekun pasha da shugaban gwamnatin Jamus ke kai wa ziyara. Kasar tana bin tsarin demokradiyya mai jam’iyyu barkatai ko da yake a daya bangaren tana fama da mummunan talauci kuma tana cikin rukunin kasashe ‚yan rabbana ka wadata mu a tsakanin kasashe masu tasowa. Kasar ta saka dogon buri akan harkar yawon bude ido domin samun kudaden shiga. Amma fa masu yawon shakatawa na dari-dari da wannan kasa sakamakon garkuwar da aka sha famar yi da baki maziyarta a cikin shekarun 1990. A yau da ranan nan aka shirya Schröder zai yi balaguron cibiyar birnin San’a’a mai dadadden tarihi. A dai ‚yan shekarun baya-bayan nan ana daukar nagartattun matakai domin kare lafiya baki dake kai ziyara wannan kasa, inda a shekarar da ta gabata ma’aikatar harkokin wajen Jamus ta janye gargadin da ta gabatar ga ‚yan kasar dangane da kurarin kai ziyara kasar Yemen. Fadar mulki ta San’a’a na daukar tsauraran matakai domin murkushe masu zazzafan ra’ayi. To sai dai kuma kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na kokawa cewar gwamnati na amfani da manufar yaki da ta’addanci ne domin karya alkadarin ‚yan adawa dake sukan lamirin manufofinta.