1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Sudan: Scholz zai tafi Afirka

Philipp Sandner BAZ/ZUD
May 3, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai kai ziyarar aiki yankin kahon Afirka a ranar Alhamis domin inganta dangantakar kasashen Jamus da Habasha da duba hanyoyin da za a kawo karshen rikicin sojoji a Sudan.

https://p.dw.com/p/4QqRU
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Wannan ita ce ziyara karo na biyu da Olaf Scholz ke kai wa kasashen Afirka tun bayan da ya zama shugaban gwamnatin Jamus. A ziyarar ta kwanaki biyu da ake sa ran zai fara a ranar Alhamis shugaban zai ziyarci kasashen Habasha da Kenya.

Baya ga duba rikicin Sudan, Scholz, zai yi magana da shugabannin wadannan kasashen a  kan yaki da yunwa da sauyin yanayi da hadin kan tattalin arziki gami.

 A cewar Jurgen Cosse dan jam'iyyar SPD ta Shugaba Scholz, wannan ziyara na da matukar muhimmanci wacce ke aikewa da babban sako.

''Addis Ababa ne shelkwatar kungiyar Tarayyar Afirka. Ina da tabbacin al'ummar Afrika sun san yadda shugaban ke son ci gaban nahiyar" in ji Mr. Cosse
Scholz zai fara yada zango a kasar Habasha, inda a baya dangantakar kasashen biyu ta yi tsami bayan kwashe shekaru biyu ana gwabza fada tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Tigray. Yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwamban bara ce ta maido da martabar firaminista Abiy Ahmed a idon hukumomin Berlin.

Masana na ganin yunkurin mahukuntan Jamus na inganta dadaddiyar danganta da ke tsakaninsu zai bai wa kasar Habasha damar ci gaba da amfana da kasuwanci da ma tallafin da suke samu daga Jamus.