1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya za ta bada Visa ga 'yan yawon bude ido

Yusuf BalaApril 26, 2016

Wannan dai zai bude idanu na bakin su san kasar ta Saudiyya tun ma kafin bayyanar addinin Islama.

https://p.dw.com/p/1Id0i
Saudi Arabien König Salman
Sarki Salman ibn Abd al-AzizHoto: picture-alliance/AP Photo/K. Mohammed

Kasar Saudiyya za ta fara bada Visa ga baki 'yan yawon bude idanu, abin da ke kunshe cikin sauye-sauye da kasar ta sanya a gabanta kan hanyoyin da kasar za ta bi kudaden shiga su rika shigar mata.

Kasar wacce ke zama ta masu tsatstsauran ra'ayi na addini ba ta bada Visa ga masu yawon bude idanu ko da yake ta taba yin gwaji na bada Visa tsakanin shekarar 2006 zuwa 2010 inda ta rika karbar baki 25,000 a kowace shekara.

Yarima Sultan bin Salman shugaban ma'aikatar da ke lura da harkokin yawon bude idanu a kasar ta Saudiyya a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Talatan nan ya ce sassautawa a harkokin da suka shafi samun Visa ta mahajjata da masu son yawon bude idanu a kasar ta Saudiyya zai bude idanu na bakin su san kasar ta Saudiyya tun ma kafin bayyanar addinin Islama. Abin da zai kara kimar kasar a idanun baki masu ziyartarta.