1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta yi shelar tsagaita wuta a Yemen

Gazali AbdouMay 8, 2015

Hukumomin kasar Saudiyya sun yi shelar tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar a Yemen daga karfe11 na daren talata mai zuwa.

https://p.dw.com/p/1FN7a
USA Saudi Arabien Kerry bei Adel al-Jubeir
Hoto: picture-alliance/dpa/AP Photo/A. Harnik

Hukumomin kasar Saudiyya sun bada sanarwar tsagaita buda wuta a kasar Yemen. Ministan kula da harakokin kasashen waje na kasar Saudiyyar ne ya tabbatar da hakan a lokacin wata fira da manema labarai ta hadin guywa da ya yi da Sakataran harakokin kasashen wajan kasar Amirka John Kerry a yau juma'a. Wannan mataki dai ya biyo bayan wata ganawa ce da John Kerry din ya yi a birnin Paris na kasar Faransa da wakillan shugabannin kasashen yankin na Golf.

Sai dai Ministan ya ce sai daga karfe 11 na dare, na ranar talata mai zuwa ne matakin tsagaita wutar zai soma aiki gadan-gadan. Kuma zai kasance na wa'adin kwanaki biyar ne kawai da amma akan iya sabunta shi idan abokanin gabar tasu suka mutunta shi.

Yau sama da wata daya kenan dai da kasar Saudiyya dake jarorantar wani kawancan kasashen larabawa ke lugudan wuta a kasar Yeman da nufin karya lago dama kywatar milki daga mayakan kungiyar Houthi ta yan Shi'a da ta karbe milki a kasar.