1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Cin hanci ya ci kujerar kwamandan Saudiyya a Yemen

September 1, 2020

Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da sanarwar cire babban kwamandan sojojin kasar a rikicin Yemen. Matakin a cewar sarkin na Saudiyya ya biyo bayan zargin facaka da kudin kasa da ake wa babban sojan.

https://p.dw.com/p/3hrj4
Saudi Arabien König Salman bin Abdulaziz
Hoto: Getty Images/D. Kitwood

Sanarwar da ofishin Sarkin ya fitar ta ce an yi wa Labtanal-Janar Fahad bin Turki bin Abdulaziz ritaya daga aikin soja kuma ana dakon kaddamar da bincike a kansa. Wannan mataki dai acewar mahukumtan Saudiyya ya biyo bayan zargin facaka da kudin kasa da ake wa babban sojan.

Hukumar yaki da cin hanci ta Saudiyya ta Nazaha ta ce bacin wannan kwamanda akwai wasu manyan sojoji da wani gwamna a Saudiyya da ake zargi da almundahana da dukiyar kasa da ke da nasaba da yakar 'yan tawayen Houthi na Yemen.