1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta kai farmaki kan 'yan Houthis

Gazali Abdou Tasawa
May 16, 2019

Jiragen yakin rundunar kawancen kasashen Larabawa da Saudiyya ke jagoranta a kasar Yemen, sun kaddamar da hare-hare ta sama a wannan Alhamis a birnin Sana'a babban birnin kasar ta Yemen. 

https://p.dw.com/p/3IboO
Jemen Sanaa Luftangriffe der Saudis
Hoto: Getty Images/AFP/M. Huwais

Wannan hari na zuwa ne kwanaki biyu bayan da 'yan tawayen kungiyar ta Houthis ta 'yan Shi'a masu samun goyon bayan Iran suka kai wasu hare-hare da jiragen marasa matuka na drone guda bakwai kan wasu kadarorin man fetir na kasar Saudiyya, harin da Saudiyyar ta dora alhakin kai shi ga kasar ta Iran. 

A cikin wata sanarwa da ta fitar rundunar kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin kasar ta Yemen ta bayyana cewa ta kai hare-hare ta sama a wasu cibiyoyin soji kasar ta Yemen da kuma a rumbunan ajiyar makamai na kungiyar 'yan tawayen Houthis.

Hukumomin kiwon lafiya a birnin na Sana'a sun ce mutane shida sun halaka, wasu gwammai sun jikkata a cikin wadannan hare-hare.