SiyasaGabas ta Tsakiya
Ana zargin mayakan Houthi da kai hari Saudiyya
February 10, 2021Talla
Mahukuntan Saudiyya sun zargi mayakan na Houthi na kasar Yemen da hannu a harin da ya haddasa gobarar, sai dai kawo yanzu babu tabbacin hakan, babu kuma cikakken bayani kan irin asarar da aka samu na rayuka ko dukiya daga mahukuntan na Saudiyya.
Filin jirgin saman na Abha da ke kusa da kan iyakan kasar da Yemen, ya sha fuskantar hare-hare daga mayakan na Houthi, amma harin na yau, shi ne wanda aka kai da ya shafi farar hula. Tuni aka karfafa matakan tsaro tare da soke duk wani shirin tashi da saukan jirage a filin jirgin saman.
Rikicin Yemen ya kara kamari ne, bayan da Saudiyya ta jagoranci kawancen kasashen Larabawa wajen kai wa mayakan Houthi hare-hare ta sama domin ba wa gwamnatin kasar goyon baya.