1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiya ta shelanta tsagaita wuta a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarMay 7, 2015

Saudiya ta sanar da cewa za ta tsagaita wuta na tsahon kwanaki biyar a Yemen domin ba da damar kai kayan agaji ga wadanda suka tagayyara sakamakon hare-haren da take kaiwa.

https://p.dw.com/p/1FMK0
Ministan harkokin kasashen ketare na Saudiya Adel Al-Jubeir
Ministan harkokin kasashen ketare na Saudiya Adel Al-JubeirHoto: Reuters/Yuri Gripas

Ministan harkokin kasashen ketare na Saudiyan Adel al-Jubeir ne ya bayyana batun tsagaita wutar, sai dai ya ce za su tsagaita wutar ne kawai in har 'yan tawayen na Houthi da magoya bayansu sun amince suma su ajiye nasu makaman. Tuni dai sakataren harkokin kasashen ketare na Amirka John Kerry, ya yi maraba da wannan batu tare kuma da bukatar 'yan tawaen na Houthi da su bada goyon bayansu domin a samu tsagaita wutar. Saudiyan dai ta ce ta dauki matakin kai hare-hare a Yemen din ne domin kare zababbiyar gwamnatin kasar daga hannun 'yan tawayne Houthi. A baya ma dai Saudiyan ta shelanta dakatar da kai hare-hare a Yemen din sai dai ba a je ko ina ba ta yi amanta ta lashe ta hanyar ci gaba da yin luguden wuta a kasar.