1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Satar jama'a don neman kudi na karuwa a Najeriya

November 22, 2016

Garkuwa da jama'a da nufin neman kudin fansa ta ta'azzara a Najeriya, batun da ake alakanta wa da talauci da ake fuskanta a sassan kasar daban-daban wanda hakan ke zama kalubale ga tsaro.

https://p.dw.com/p/2T53v
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Yanzu haka dai sakamakon karuwar ayyukan masu garkuwa da sace-sacen mutane dan samun kudade a Kaduna ya sanya zaman zulumi da fargaba tsakanin al'ummar jihar, lamarin da ke nuni da cewa lamarin fi yadda ya ke a Kudancin kasar inda nan ne a baya ake fuskantar wannan matsala. Sannu a hankali ne dai wannan mummunar dabi'a ta sami damar gangarowa yankin Arewa kuma inda abun ya fi tsananta yanzu haka shi ne jihar Kaduna Arewa maso Yammacin kasar, sakamakon karuwar tabarbarewar rashin tsaro da tsananin talauci da rashin aikin yi da ke addabar al'umma.

Nigeria Angespannte Sicherheitslage in Yola
Hoto: DW

Kwanaki biyun da su ka gabata ne aka sace wani tsohon minista a Kaduna a gaban jami'an tsaro, bugu da kari wannan matsala ta sanya hatta manyan attajirai da kusoshin gwamnati da iyayen kananan yara a kowane lokaci zaman fargaba a cikin jihar. Tuni dai 'yan siyasa a jihar ciki kuwa har da dan majalisar dattawa na Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani su ka fara kokawa a kan karuwar wannan matsala ta garkuwa da mutane, inda ya yi kira kan a dauki matakan magance matsalar. Wannan batu dai ya sanya jama'a jin tsoron bin hanyar Birnin Gwari da ke a kan hanyar zuwa Lagos sakamakon karuwar ayyukan ‘yan fashi da makamai da sauran kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke zaune a cikin dokar daji.

Bincike dai ya nunar da cewa a kan yi ciniki ne da masu garkuwa da 'yan uwan wanda aka kama kafin a sako shi, sai dai rundinar 'yan sanda ta kasar ta na ci gaba da jaddada cewa za ta ci gaba da kokari na kawo karshen matsalar da ke neman gagarar Kundila.