Sassauta dokar yawo da makami a Isra'ila
November 18, 2014Talla
Ministan tsaron al'umma na kasar Yitzhak Aharonovitch ya ce gaba kadan a yau ne suke son aiwatar da wannan tsari sai dai zai shafi wanda ke da lasisi na mallakar bindiga ne kawai gami da sojojin da ba sa kan aiki da kuma irin jami'an tsaron nan wanda ba na hukuma ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu Falasdinawa suka hallaka wasu mutane hudu tare da raunata karin wasu a wani farmaki da suka kai wajen ibadar Yahudawa a birnin Jerusalam, harin da mahukuntan Falasdinu suka yi Allah wadai da shi.