1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deby: Shugaban kasar Chadi karo na biyar

Abdoulrazak Garba Babani/LMJAugust 8, 2016

A karo na biyar a kasar Chadi an sake rantsar da Shugaba Idriss Deby Itno a matsayin shugaban kasar, duk kuwa da nuna kin amincewa daga bangaren 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/1Jddg
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby: Shugabanci a karo na biyar
Shugaban kasar Chadi Idriss Deby: Shugabanci a karo na biyarHoto: DW/D. Blaise

A wannan Litinin din takwas ga watan Agusta na 2016 ne dai Shugaba Idriss Deby na Chadin ya yi rantsuwar kama aiki a karo na biyar bayan da ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Afrilun da ya gabata. 'Yan adawar kasar ta Chadi dai na ci gaba da suka da kuma tirjiya dangane da sakamakon zaben da ya bai wa Deby nasara da suka ce haramtacce ne. Rantsuwar kama aikin ta Deby na zuwa ne kwana guda bayan da guda daga cikin 'yan adawar ya rasa ransa yayin wata zanga-zanga da 'yan adawar suka gudanar. A yayin da yake rantsuwar kama aikin na tsahon wasu shekaru biyar masu zuwa a karo na biyar, Deby ya ayyana knsa a matsayin shugaba ga baki dayan al'ummar Chadi tare da shan alawashin yakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka addabi kasar da ma sauran kasashen da ke makwabtaka da ita. Daga cikin shugabannin kasashe 14 da suka halarci rantsuwar ta Shugaba Idriss Deby dai har da na Najeriya da Nijar, wadanda su ma ke fama da rikicin Boko Haram. Mai shekaru 64 a duniya, Deby ya fara mulkin kasar ta Chadi Faransa tai wa mulkin mallaka ne tun a shekara ta 1990. Jagoran adawar kasar da ya yi takara tare da Deby a zaben shugaban kasar da ya gabata, Saleh Kebzabo ya sha alwashin ci gaba da nuna adawarsa ga sakamakon zaben da ya bai wa Deby nasara.