1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren harkokin wajen Amirka a Najeriya

Umaru AliyuJanuary 25, 2015

Amirka ta baiyana bukatar gudanar da kyakkyawan zabe a Najeriya, wanda zai taimaka ga shawo kan rikicin Boko Haram da ya addabi kasar da kasashe makwabta.

https://p.dw.com/p/1EQJC
Kerry in Lagos, Nigeria
Hoto: Reuters/Akinleye

A wani mataki da ba a saba gani ba, ranar Lahadi sakataren harkokin wajen Amirka, John Kerry ya ziyarci Najeriya, inda a birnin Lagos, ya tattauna a game da halin da kasar take ciki, musamman shirye-shiryen zaben shugaban kasa ranar 14 ga watan Fabrairu da batun tsaro, inda kasar take fuskantar kalubale mai yawa daga mayakan kungiyar Boko Haram. Ziyarar dai tazo ne a ranar da rahotanni suka tabbatarda cewar dakarun kungiyar ta Boko Haram sun kai hari a garin Maiduguri da kewayensa, inda ma suka kwace garin Munguno da barikin sojojin dake cikiinsa.

John Kerry ya gana a birnin na Lagos da shugaban kasa, Goodluck Jonathan da dan takara na babbar jam'iyar adawa ta APC, Janar Muhammadu Buhari. Daga baya, lokacin ganawa da manema labarai, John Kerry ya baiyana bukatar gudanar da zabubbukan Najeriya lami-lafiya, cikin kwanciyar hankali, ba kuma tare da an daga lokacin gudanar da zabubbukan ba, kamar yadda wasu suke bada shawarar yi. Kerry yace nahiyar Afirka da duniya baki daya tana zura ido ga Najeriya, wadda ita ce democradiya mafi girma a nahiyar Afrika, domin zama abin misali a game da gudanar da zabe na-gari. Sakataren harkokin wajen na Amirka yace matsalar Boko Haram ba za a shawo kanta ba, sai idan kasatr ta Najeriya ta gudanar d a zabe mai karbuwa, tare da aringizon kuri'u ko magudi da satar akwatunan zabe ba.

Dangane da batun tsaro, sakataren harkokin waje John Kerry yace Amirka tana ci gaba da goyon bayan Najeriya ta fannoni da dama a kokarinta na shawo kan batun rashin tsaro a wannan kasa. Kerry yace Najeriya tana hada kai matuka da Najeriya kann batun na tsaro, ko da shike wannan hadin kai ba ya gudana sosai kamary adda, yan Najeriya suke bukatarsa. Ya kara da cewar aiyukan ta'addanci yana karuwa ne sakamakon karuwar rashin aikin yi tsakanin mkatasa, wadanda babu wuyan jan hankalinsu ya zuwa ga kungiyar ta Boko Haram.