1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a Brazil

October 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buhc

Hukumar zaɓe a Brazil ta bayana sakamakon zaɓen shugaban ƙasa,, zagaye na farko, da aka gudanar jiya, a fadin ƙasar baki ɗaya.

Kamin shirya wannan zaɓe, ƙiddidigar jin ra´ayin jama´a, ta nunar da cewa, shugaban ƙasa mai ci yanzu, Luiz Inacio Lula Da Silva, za shi tazarce tun zagaye na farko, ta la´kari da farin jinin da ya samu daga al´ummar ƙasa.

To saidai sakamakon da hukumar zaɓen ta bada, ya tabbatar da shirya zagaye na 2, ranar 29 ga watan da mu ke ciki, inda za a fafata, tsakanin Lula Da Silva, da Geraldo Alckmin da ya zo sahu na 2.

Sakamakon farko, ya ba Shugaba Lula, kimanin kashi 49 bisa 100, na jimillar ƙuri´un da aka a kaɗa, a yayin da abokin hamayar sa, ya samu kusan kashi 41 bisa 100.

A jimilce, mutane million 125 ne ,na Brazil su ka zaɓi shugaban ƙasa, da kuma yan majalisun taraya da na jihohi.