1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakacin 'yan sanda ya janyo cin zarafin mata a Cologne

Helena Baers/ Umaru AliyuJanuary 11, 2016

Ministan cikin gidan jihar North-Rhein Westfalia Ralf Jäger ya dora laifi mai yawa kan jami'an tsaron Cologne a lamarin nan na cin zarafin mata a babbar tashar jirgin kasar birnin.

https://p.dw.com/p/1HbTl
Deutschland Köln Demonstrationen Pegida Gegendemonstranten
Hoto: picture-alliance/dpa/O.Berg

Lokacin gabatar da rahoton gaban majalisar dokoki da ke Duesseldorf shalkwatar jihar ta North-Rhine Westfalia, ministan cikin gida Ralf Jäger ya ce wasu al'amura biyu ne suka zama masu muni tattare da abin da ya faru ranar 24 ga watan Disamba 2015 da dare a Cologne. Abu na farko shi ne 'yan sanda sun kasa daukar matakin neman karin ma'aikata da za su taimaka domin shawo kan abin kunyar na cin mutuncin mata a tashar. Sai kuma abu na biyu, inda 'yan sandan suka yi kokarin boye wa bainar jama'a abin da ya faru da kuma sakamakon binciken da aka yi kan wannan al'amari.

Tun a makon da ya gabata, Jäger ya baiyana zargin cewar 'yan sanda suna da babban laifi kan abin da ya faru, inda baki 'yan ci rani da 'yan gudun hijira akalla 1000 daga kasashen Larabawa da Arewacin Afirka suka rika cin mutuncin mata da suka taru domin bikin jajiberin sabuwar shekara. A sakamako wannan zargi ne Jäger ya tilasta wa shugaban 'yan sandan birnin Cologne, Wolfgang Alber ya yi ritaya, inda ya ce:

"Wannan kudiri da na dauka ya zama wajibi a yanzu, saboda tilas ne a dauki irin wannan mataki domin sake dawo da martaba da darajar rundunar 'yan sandan Cologne tsakanin al'ummar birnin, musmaman tattare da wasu manyan bukukuwa da ke tafe nan gaba a Cologne. Rundunar 'yan sandan yanzu dai tana da gagarumin aiki a gabanta na bincike da gano gaskiyar abin da ya faru ranar jajiberin sabuwar shekarar, da kuma matakan hukunci da za ta dauka. Jama'a suna son sanin ainihin abin da ya faru a wannan dare, su wane ne suka aikata haka da kuma yadda hana aukuwar irin wannan al'amari nan gaba."

Za a hukunta duk wanda aka samu da laifi

Ministan cikin gida na North-Rhein Westfalia Ralf Jäger ya musunta zargin cewar wai 'yan sandan na Cologne sun amsa umurni ne da ya nemi su boye duk wani bayani tattare da abin da ya faru, ko kuma ainihin daga asalin wadanda suka aikata laifin na cin zarafin mata. Tun da farko sai da ministan ya shaida wa kwamitin al'amuran cikin gida na majalisar dokoki a Duesseldorf cewar a binciken da za a yi domin gano gaskiyar abin da ya faru, babu wani abu, ko wani mutum da za a ji shakkar taba shi. Batun siyasa ba zai shigo cikin al'amarin ba, domin kuwa matan da wannan abin kunya ya rutsa da su, sun cancanci a bi masu kadin al'amarin.

Deutschland Ralf Jäger Innenausschuss NRW-Landtag
Ralf JägerHoto: Reuters/I. Fassbender

Sabuwar muhawara kan 'yan gudun hijira

Al'amuran da suka faru a Cologne din dai, sun tayar da sabuwar muhawara game da matsayin 'yan gudun hijira da yiwuwar ba su mafakar siyasa a nan Jamus, musamman saboda zargin cewar da yawa daga cikin wadanda ake zargin sun ci mutuncin matan 'yan gudun hijira ne.

Yayin da 'yan siyasa suke muhawarar ko ya kamata wadanda aka samu da laifin su rasa 'yancinsu na samun mafakar siyasa, shugabar gwamnati, Angela Merkel ta ce hakan yana daga cikin al'amuran da ake nazari kansu.

CDU-Vorsitzende Angela Merkel Klausurtagung CDU Mainz
Ana nazari kan matsayin 'yan gudun hijira a Jamus- Angela MerkelHoto: picture-alliance/dpa/F.von Erichsen

"Hakan yana nufin 'yan gudun hijiran suna iya rasa 'yancinsu na samun mafakar siyasa ko a duba takardunsu na neman zama a Jamus a matsayin 'yan gudun hijira idan har aka same su da laifi, aka kuma zartas masu da hukunci ko dai na dauri ne a gidan kaso ko kuma daurin talala."

Ministan cikin gida na jihar North-Rhein Westfalia Ralf Jäger ya ce yana sane da cewar bincike kan wannan al'amari da ya faru a Cologne zai zama abu ne mai matukar wahala, musmaman saboda yawan wadanda ake zargi da aikata laifin. Abin da ya rage shi ne a ga yawan wadanda za a kama bisa zargin cin mutuncin matan. Duk da haka, ya yi gargadi a game da daukar baki gaba daya a matsayin masu aikata laifuka. Idan aka yi haka, wadanda za su ci ribar hakan su ne kungiyoyi masu kyamar baki, wadanda ba sa son kwararowar 'yan gudun hijira zuwa Jamus.