1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar tattaunawar zaman lafiyar Sudan ta Kudu

Abdul-raheem Hassan
February 5, 2018

Kasashe masu fada a ji sun bukaci bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu, da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da za ta kawo kashen rikicin da ya haifar da 'yan gudun hijira mafi yawa a nahiyar Afirka.

https://p.dw.com/p/2s9A3
Äthiopien Friedensgespräche Süd Sudan
Hoto: picture alliance/dpa/abacaM. W. Hailu

Sabon yunkurin tattaunawar da aka sake shiga a birnin Addis Ababa na Habasha, ya zo ne bayan da Amirka ta dau matakan haramta sayar wa Sudan ta Kudu makamai, tare da barazanar karin wasu tsauraran matakai. Amirka ta kuma bukaci sauran kasashe da su bi sahun daukar irin wannan mataki na ladabtar da Sudan ta Kudun.

Rashin hakuri da zargin tsokana tsakanin bangaren gwamnati da 'yan tawaye, ya rusa yarjejeniyar da aka cimma a karshen shekarar 2017 a birnin Addis Ababa bayan da aka fara samun hare-hare kan bangarorin biyu.