SiyasaJamus
An kafa sabuwar gwamnati a Libya
March 15, 2021Talla
Ana dai fatan gwamnatin da aka samar ta hanyar zaman sassanci na Majalisar Dinkin Duniya da bangarorin da ba sa ga maciji da juna ya samar da tudun mun tsira ga kasar don kawo karshen shekaru 10 na rikici tun bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta jagoranci hanbarar da gwamnatin shugaba Muammar Gaddafi.
Sabuwar gwamnatin za ta maye gurbin tsohuwar gwamnatin hadaka ta Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin Tripoli karkashin jagorancin dakarun da ke goyon bayan Khalifa Haftar. Kazalika gwamnatin za ta kunshi mataimakan Firamininistoci biyu da ministoci kimanin 30 da sauran manyan mukaman gwamnati.